Ofishin hukumar ta OCHA ya bayyana cewa, a shekarar 2017 da ta gabata, an samu karuwar rahotanni kisan ma'aikatan agaji mafi yawa, inda aka kashe ma'aikatan agaji 28. MDD dai ta ce irin wadannan kashe-kashe sun hada da na ma'aikatan agaji, ko fashi da makami, kwashe kayayyakin agaji da barazana ko tursasawa, kuma galibi sun faru ne a yankunan Juba, Rubkona da Wau. (Ibrahim)