in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 15 ne aka kashe a wani tashin hankali a arewa maso gabashin Najeriya
2018-03-04 13:08:33 cri

A kalla mutane 15 ne aka tabbatar da mutuwarsu kana wasu da dama suka jikkata a sakamakon wani sabon fada da ya barke a garin Mambilla dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, wasu mazauna yankin da 'yan sandan wurin sun tabbatar da afkuwar lamarin jiya Asabar.

Jami'an 'yan sandan yankin sun bayyana cewa, tashin hankalin ya barke ne tun ranar Alhamis, sakamakon rashin fahimtar juna da ta kaure tsakanin wani makiyayi da manomi a garin na Mambilla, garin dai ya kasance daya tilo a kasar ta yammacin Afrika da ake sarrafa ganyen shayi na highland tea wanda ake noma shi a yankin na jihar Taraba.

Kakakin rundunar 'yan sanda David Misal, ya bayyana cewa akwai gidaje da dama da aka kone su kurmus kana an kashe shanu a lokacin barkewar tashin hankalin.

Misal ya fadawa 'yan jaridu cewa, an tura bataliyar 'yan sanda da sojoji don tabbatar da doka da oda a yankin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China