Rahoton jaridar Vanguard na kasar ya ruwaito cewa, a rubu'i na karshe na shekarar bara, yawan jarin da Najeriya ta samu daga ketare ya kai dala biliyan 5.3, wanda ya ninka kusan sau uku idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a shekara ta 2016, ciki har da dala biliyan 3.5 da aka zuba a kasuwar hannayen jari.
Alkaluman sun yi nuni da cewa, tattalin arzikin Najeriya ya farfado sannu a hankali a bara, kuma masu zuba jari na kasashen waje sun kara samun kwarin-gwiwa game da tattalin arzikin kasar.(Murtala Zhang)