Wani malamin jami'ar TUT dake Afirka ta kudu, ya bayyana saukar da shugaban kasar Jacob Zuma ya yi daga jagorancin kasar, a matsayin wani mataki da zai kawo daidaito a fagen siyasar kasar.
Malamin jami'ar mai suna Ricky Mukanyaradzi Mukonza, ya bayyana hakan ne jiya Laraba yayin zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, yana mai cewa hakan zai bada damar bunkasa tattalin arziki, da kuma kyautata yanayin siyasar kasar.
Mr. Mukonza, ya kara da cewa, jam'iyyar ANC za ta samu sabon tagomashi, a fannin siyasa da tattalin arziki sakamakon saukar shugaban kasar.
Ya ce ci gaba da kasancewar Zuma shugaban Afirka ta kudu zai cutar da kasar, duba da yadda gwamnatin sa ke ci gaba da fuskantar zarge zarge na cin hanci da rashawa, matakin da ke kore masu sha'awar zuba jari.
Zuma dai na fuskantar kalubale daban daban, kuma mai yiwuwa ma ya fuskanci tuhuma a kotu bisa zarge zarge da dama.
Mr. Mukonza ya ce ana sa ran sabon shugaban Afirka ta kudu zai dauki matakai na sake gina tsarin jagorancin kasar, musamman ma fannin yaki da rashawa.(Saminu Alhassan)