Majalissar dokokin kasar Afirka ta kudu ta zabi jagoran jami'iyyar ANC mai mulkin kasar, Cyril Ramaphosa a matsayin sabon shugaban kasa. Da wannan mataki Ramaphosa ya zamo shugaban Afirka ta kudu na 5 a tarihi.
An zabi Cyril Ramaphosa ne bayan da shugaba Jacob Zuma ya amince ya yi murabus daga mukamin shugabancin kasar a daren ranar Laraba.
Cikin jawabin sa na amincewa da zaben, Mr. Ramaphosa ya godewa 'yan majalissar dokokin kasar bisa abun da ya kira, dama da suka ba shi ta bautawa al'ummar Afirka ta kudu. Kaza lika ya alkawarta tabbatar da gudanar da ayyukan sa yadda ya kamata.
Ana sa ran sabon shugaban zai gabatar da jawabi ga al'ummar kasar a Jumma'ar nan.(Saminu Alhassan)