in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilan kasa da kasa sun tattauna kan manufofin Sin a gun taron hadin gwiwar biyan haraji na duniya karo na farko
2018-02-15 13:25:37 cri
An bude taron hadin gwiwa game da biyan haraji na duniya karo na farko a cibiyar MDD a ranar 14 ga wata, inda wakilan kasa da kasa suka bayyana cewa, manufofin haraji na kasar Sin, sun taimakawa wajen nuna goyon baya da sa kaimi ga samun bunkasuwa mai dorewa, wanda ya kamata kasashe masu tasowa su yi koyi daga fasahohin Sin.

Za a shafe kwanaki uku ana gudanar da wannan taro, kuma jami'an sassan tattara haraji, da wakilai daga bangarori daban daban na kasa da kasa kimanin 450 sun tattauna, kan yadda manufofin haraji ke sa kaimi ga cimma burin samun bunkasuwa mai dorewa.

A yayin taron, shugaban hukumar harkokin haraji ta kasar Sin Wang Jun, ya yi bayani game da ayyuka da manufofin da Sin ta aiwatar na goyon baya ga samun bunkasuwa mai dorewa. Wang Jun ya bayyana cewa, Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kungiyoyin kasa da kasa, da hukumomin haraji na kasashen duniya, don samar da yanayin hadin gwiwa da samun moriyar juna na duniya a wannan fanni.

Sakataren gudanarwa na dandalin tattaunawa kan sarrafa haraji na Afirka ya bayyana cewa, a cikin shekaru 5 da suka gabata, Sinawa fiye da miliyan 66 sun fita daga kangin talauci, inda kudin da aka shigar daga fannin haraji ya taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da hakan. Ya ce ya kamata kasashe masu tasowa su yi koyi da wadannan fasahohi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China