in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na MDD ya yi kira ga kasashen duniya su karfafa hadin kai domin magance kalubalen da ake fuskanta
2018-02-17 13:09:28 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira da karfafa aminci da hadin kai wajen shawo kan kalubalen da ake fuskanta da barazanar tsaro da rikice-rikicen da ke kara shafar juna

Da yake jawabi ga babban taron tsaro karo na 54 da aka kaddamar jiya Jumma'a a birnin Munich na kudancin Jamus, Antonio Guterres ya ce a yanzu ne aka fi bukatar hadin kan kasashe sama da kowane lokaci, ya na mai cewa matsalolin da ake fuskanta a duniya na bukatar hadin kan baki dayan kasashen duniya wajen samo mafita.

Guterres wanda ya ce an dan samu ingantuwar al'amura ta fuskar shawo kan rikice-rikice musamman a yankin gabas ta tsakiya a bara, ya tunatar da cewa an samu ingantaccen sauyi a yankin gabsa ta tsakiya, inda a baya al'mura suka lalace sanadiyyar rikice-rikice dake da alaka da juna.

Ya ce maimakon kokarin warware matsalar a rarrabe, kamata ya yi a cimma buri na bai daya tare da tabbatar da hadin kan kwamitin sulhu na MDD game da batun gabas ta tsakiya, musammam batutuwan da suka shafi Syria.

Da yake jawabi game da kawar da makaman nukiliya a zirin Korea, sakatare janar din ya yi maraba da ingantuwar al'amura game da dangantakar Korea da aka samu cikin makonnin baya-bayan nan.

Har ila yau, ya jadadda cewa muhimmin batu shi ne, kawar da makaman nukiliya, wanda ke bukatar hadin kan dukkan bangarorin da ya shafa. Game da wannan ne kuma ya bukaci Amurka da Koriya ta arewa su hada hannu wajen gudanar da tattaunawa mai ma'ana. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China