in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cutar zazzabin Lassa ta hallaka rayuka 72 a Najeriya
2018-03-01 12:34:56 cri
Cutar annobar zazzabin Lassa ta hallaka rayukan mutane masu yawa, inda alkaluma suka nuna ta kashe mutane 72 bayan da aka gwada mutane 317 da aka yi amannar sun kamu da cutar, hukumar lafiya ta duniya WHO ne ta tabbatar da hakan a jiya Laraba.

Kwayoyin cutar mai saurin kisa ta yadu ne a jahohin kasar 18, tun bayan da aka samu rahoton bullar cutar a cikin sabuwar shekara. Kimanin mutane 2,845 da ake kyautata zaton sun kusance wadan da suka kamu da cutar ne aka sanyawa ido a fadi kasar, kamar yadda hukumar ta WHO ta rawaito daga hukumar magance bazuwar cutuka ta kasar (NCDC).(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China