Faki, ya bayyana a taron kolin majalisar gudanarwar AU karo na 18, a matsayin wani bangare na taron kolin kungiyar ta AU game da batun tsarin na AfCFTA. Ya ce a bisa mahangar shirin a matakin kasa da kasa, da kuma irin koma bayan da huldar gamayyar kasashen ke fuskanta, da irin goyon bayan da wasu mutane ke nunawa, ya sanya jagororin kungiyar suka yanke shawarar kaddamar da wannan tsarin mai matukar muhimmanci.
A lokacin da sauran kasashen duniya suke kokarin hada kansu da yin aiki tare wajen kare matsayin bukatunsu, Afrika ba ta da wani zabi da ya wuce ta yi gaban kanta wajen kaddamar da wannan tsarin.
Shugaban na AU ya ce, har yanzu akwai sauran batutuwan da ake son cimmawa, musamman batun yanayin kafa sakatariyar tsarin na ciniki marar shinge, da adadin ka'idojin da ake bukatar cika su kafin shiga yarjejeniyar shirin na AfCFTA. (Ahmad Fagam)