in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban AU: Za'a rattaba hannu kan yarjejeniyar yin ciniki mai 'yanci ta kasashen Afrika a watan Maris
2018-02-13 11:25:51 cri
Shugaban kasar Rwanda kana shugaban gudanarwar kungiyar tarayya Afrika AU, Paul Kagame, ya bayyana cewa, za'a rattaba hannu kan yarjejeniyar yin ciniki cikin 'yanci (CFTA) mai dadadden tarihi, a watan Maris a Kigali, babban birnin kasar Rwanda.

Ana sa ran za'a rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a babban taron kolin kungiyar ta AU, Kagame ya furta hakan ne a babban taron shekara shekara na kamfanonin Inshora na Afrika (FANAF) karo na 42, wanda aka bude a ranar Litinin a Kigali.

Shugaban na Rwanda ya ce, wannan yarjejeniya ce mai cike da tarihi wadda ta shafe kusan shekaru 40 da kulla ta, kuma ta shafi muhimman batutuwan da suka kunshi cigaban nahiyar da hadin kanta.

Ya ce, cigaban da kasashen Afrika za su iya samu ta fuskar 'yanci a harkokin cinikayya nan da shekaru masu zuwa, zai kasance a matsayin wasu sabbin damammaki ne da kamfanonin Afrikan za su samu na yin takara da gogayya a fadin nahiyar.

Kagame ya ce za su daidaita dokokinsu, kuma za su aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar ta CFTA domin samun alfanu ta fuskar cigaban tattalin arziki wanda mutanen nahiyar ke matukar bukatarsa. Shi dai Kagame, ya bukaci dukkannin kasashen na Afrika da su bada goyon baya don aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata.(Ahamd Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China