Yayin da kasar ke tunkarar zagaye na 2 na zaben shugaban kasar cikin makonni 2 masu zuwa, tarayyar, ta yi kira ga masu ruwa da tsaki kan harkokin zabe, musammam 'yan takarar jam'iyyun SLPP da na APC, su tabbatar da dorewar zaman lafiya tare da yin dukkan mai yiwuwa wajen tabbatar da an yi nasarar kammala zaben.
Ya kara da cewa, kudurin AU shi ne mara baya ga karfafa tsarin demokradiyya a Sierra Leone da sauran kasashe mambobinta, ta hanyar gudanar da sahihin zabe mai cike da adalci da kwanciyar hankali. ( Fa'iza Mustapha )