in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar tarayyar Afrika za ta kaddamar da kasuwanci marar shinge
2018-03-11 13:29:50 cri
Kungiyar tarayyar Afrika AU ta yanke shawarar kaddamar da tsarin ciniki cikin 'yanci, Moussa Faki Mahamat, shugaban hukumar gudanarwar kungiyar ne ya tabbatar da hakan.

Ya ce a taron kolin kungiyar karo na 31 a watan Janairu da aka gudanar a Addis Ababa, sun cimma wasu kudurori masu muhimmancin gaske, musamman batun kafa tsarin kasuwanci marar shinge wato AFTZ, wanda zai kasance cikin manyan ajandodin taron kolin kungiyar na nan gaba wanda za'a gudanar a ranar 21 ga watan Maris a Kigali na kasar Rwanda, baya ga batun tsarin fasfo na Afrika, da kuma batun kyautata sufurin jiragen sama a nahiyar, jami'in na AU ya bayyana wa 'yan jaridu a lokacin da ya sauka a filin jirgin saman kasa da kasa na Algiers a lokacin ziyarar aiki.

Ya kara da cewa, an gayyaci dukkan shugabannin kasashen da na hukumomin Afrikan taron kolin kungiyar na Kigali inda ake sa ran za'a rattaba hannu kan batun yarjejeniyar ta AFTZ.

Wannan shi ne karon farko da Faki Mahamat ya kai ziyarar aiki tun bayan da aka zabe shi a matsayin shugaban kungiyar ta AU.

Haka kuma, zai yi wata ganawa da manyan jami'an kasar Algeria domin yin musayar ra'ayoyi game da wasu muhimman batutuwa dake faruwa a Afrikar a halin yanzu, da kuma yadda za'a kyautata dangantaka tsakanin kasar ta Algeria da kungiyar tarayyar Afrika. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China