in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin kasashen Afrika za su gana domin nazarin dokokin kafa yankin ciniki cikin 'yanci
2018-03-09 12:51:07 cri
Ministocin kasashen Tarayyar Afrika AU, sun fara wani taro a jiya Alhamis, domin kammala tattaunawa game da dokokin kafa yankin cinikayya cikin 'yanci a nahiyar Afrika.

Taron na yini biyu da ake yi a Kigali babban birnin kasar Rwanda, na gudana ne gabanin taron AU kan yankin na cinikayya da zai gudana daga ranar 17 zuwa 21 ga watan nan da muke ciki a birnin na Kigali.

A cewar ministan ciniki na Rwanda Vincent Munyeshyaka, abu ne mai muhimmanci a gaggauta cimma yarjejeniya game da yankin, domin tabbatar da burin nahiyar na samar da kasuwar bai daya ga kasashenta. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China