A karon farko, a yau Litinin, sabon ministan kimiyyya da fasaha na kasar Sin Wang Zhigang, ya bayyana a gaban jama'a, a yayin zama na farko na babban taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 cewa, za a yi kokarin ganin kasar Sin ta ba da gudummowa a duniya ta fuskar kimiyya da fasaha.
A yayin da ya amsa tambayoyin manema labaru, Mr. Wang Zhigang ya ce, a matsayinsa na sabon ministan harkokin kimiyya da fasaha na kasar Sin, zai mai da hankali matuka kan yadda kimiyya da fasahar kasar Sin za su kara ba da sabuwar gudummowa, ta zamanintar da kasar.
Ya kara da cewa, wajibi ne a raya kimiyya da fasaha ta zamani, a kokarin biyan bukatun manyan tsare-tsaren kasa, da bunkasa tattalin arziki, da zamantakewar al'ummar kasar. Ya ce dole ne a samar da kyakkyawan muhalli, inda karin masu ayyukan kimiyya da fasaha, da sassa daban daban na kasar, za su shiga cikin ayyukan kimiyya da fasaha. Sa'an nan wajibi ne a samar da kyakkyawan yanayi, na girmama kwararru da ayyukan kimiyya da fasaha. (Tasallah Yuan)