in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gyaran kundin tsarin mulkin kasar Sin ya shaida yadda tsarin siyasa na kasar ke tafiya tare da zamani
2018-03-12 16:08:18 cri
An zartas da gyaran kundin tsarin mulkin kasar Sin yayin taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 a jiya Lahadi. Ma'aikaciyar sashen nahiyar Afirka ta kungiyar GRI Wadeisor Rukato, na ganin cewa, gyaran kudin tsarin mulkin kasar Sin ya shaida yadda tsarin siyasa na kasar ke tafiya tare da zamani. Tsarin siyasa na kasar Sin yana da inganci musamman idan aka kwatanta shi da na sauran kasashen duniya.

Wadeisor Rukato wadda 'yar asalin kasar Zimbabwe ce, ta bayyana cewa, bunkasar kasar Sin cikin sauri musamman a fannin tattalin arziki kwarin gwiwa ce ga kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga a duniya, wadanda suka koyi fasahohi daga ci gaban tattalin arzikin Sin, tare da tsara manufofin raya kasashensu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China