Wu Heng ya bayyana cewa, a cikin shekaru 5 da suka gabata, zaunannen kwamitin majalisar karo na 12 ya duba tare da zartas da dokar tabbatar da jin dadin al'umma ta fannin al'umma, da dokar raya sana'ar fim, da dokar dakin karatun jin dadin al'umma, sa'an nan ya kuma gyara dokokin kare kayayyakin tarihi da bayanan da aka adana, ta haka an kyautata yanayin dokokin al'adu na kasar. Sabbin dokokin al'adun da aka tsara sun jaddada jagorancin gwamnatin kasar, tare kuma da sa kaimi ga bangarori daban daba na al'umma da su shiga ayyukan a wannan fanni, har wa yau sun kyautata wasu ka'idoji a wannan fanni. (Zainab)