in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kafa dokokin kiyaye muhalli ne ta yin la'akari da tabbatar da moriyar jama'a
2018-03-12 13:59:31 cri
Membar kwamitin kiyaye muhalli da albarkatun halittu ta zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Lv Caixia ta bayyana a yau Litinin cewa, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 12 ya bullo da wasu dokoki game da kiyaye muhallin halittu, don kare muradun jama'a, da warware matsalolin gurbacewar iska da ruwa da sauransu bisa halin da ake ciki a kasar Sin.

A yayin taron manema labaru na zaman taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 da aka gudanar, Lv Caixia ta bayyana cewa, akwai wasu dokoki 18 da zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 12 ta kafa da suka shafi kiyaye muhallin halittu, kuma yayin da aka tsara dokokin ne an fi mai da hankali a kan kyautata tsarin a wannan fanni, da hada wannan batu da manufofin raya kasa da kula da muradun al'ummar kasar, da kuma yin kokarin bullo da tsarin magance gurbacewar muhalli na kasar.

Game da yaki da gurbacewar iska kuwa, Lv Caixia ta bayyana cewa, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a wannan karo ya maida hankali ga ayyukan kafa dokoki, da warware matsaloli bisa halin da ake ciki a kasar, kuma an samu wasu nasarori. Hakazalika kuma, ta ce, yaki da gurbacewar yanayi shi ne aikin da za a dade ana gudanarwa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China