Bisa sunayen da firaministan majalisar gudanarwar kasar Sin Li Keqiang ya gabatar, an kuma jefa kuri'a don nada ministoci da shugabannin kwamitoci da gwamnan babban bankin kasar Sin da shugaban hukumar binciken kudi ta kasar, gami da babban sakataren majalisar gudanarwar kasar.
Bugu da kari, ta hanyar jefa kuri'a, aka zartas da sunayen shugabannin kwamitocin majalisar NPC, da mataimakan shugabannin da ma mambobin majalisar.
Har ila yau, yayin zaman na yau, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umurnin nada mambobin majalisar gudanarwar kasar bisa kudurin da taron NPC ya tsayar.
Bayan kammala ajandu daban-daban na cikakken zama taron NPC na yau, mataimakan firaminista da mambobin majalisar gudanarwar kasar sun yi rantuwar kama aiki a gaban kundin tsarin mulkin kasar Sin. (Kande Gao)