A yayin zaman taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 da da ke gudana a nan birnin Beijing, a yau Lahadi an jefa kuri'u inda aka zabi Li Keqiang a matsayin firaministan kasar Sin, shi kuwa Yang Xiaodu ya zama daraktan kwamitin sa ido na kasar Sin.
Baya ga haka, an zabi Xu Qiliang da Zhang Youxia don su zama mataimakan shugaban kwamitin tsakiya na aikin soja, kana an zabi Zhou Qiang ya jagoranci kotun koli, yayin da Zhang Jun ya zama shugaban hukumar koli ta gabatar da kararraki. Bayan an kammala taron, bi da bi ne Li Keqiang da Yang Xiaodu da sauran jami'an da suka ci zaben sun yi rantsuwa da kundin tsarin mulkin kasar. (Bilkisu)