An zabi shugaban ne yayin cikakken zaman taro karo na biyar, cikin zagayen farko na taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 a nan birnin Beijing.
Haka kuma, an zabi Li Zhanshu a matsayin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 da kuma Wang Qishan a matsayin mataimakin shugaban jamhuriyar jama'ar kasar Sin.
Bayan cikakken zaman taron karo na biyar, an yi bikin rantsuwa da kundin tsarin mulkin kasar. Kuma wannan shi ne karon farko da shugabannin kasar Sin suka yi rantsuwa da kundin tsarin mulkin kasa a wajen taron majalisar wakilan jama'ar kasar, tun bayan fara aiwatar da tsarin rantsuwa da kundin tsarin mulkin kasar Sin. (Maryam)