Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya bayyana cewa, lashe zaben da shugaba Xi ya yi ya nuna cewa jama'ar kasar Sin na cike da imani kan hangen nesa da basira da Xi ke da ita game da tafiyar da harkokin kasar ta Sin da ma kasa da kasa. Ya ce, ya yi imanin cewa, za a cimma gagarumar nasara kan taron kolin Beijing na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afirka da za a shirya a watan Satumbar bana, hakan zai taimaka wajen ciyar da dangantakar abokantaka dake tsakanin bangarorin biyu gaba.
A nasa bangaren, shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya bayyana cewa, a matsayinsa na shugaba mai gaskiya kuma wanda ke kokarin sauke nauyin dake wuyansa, shugaba Xi ya samu gogon baya sosai daga jama'arsa. Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keïta ya ce, lashe zaben zama shugaban kasa da Xi Jinping ya yi shaida yadda jama'ar kasar suka amince da kwarewarsa ta gudanar da harkokin kasar da kyawawan halayensa wajen hidimtawa jama'ar Sinawa. (Bilkisu)