Yau da safe ne aka gudanar da zama na tara na taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin(NPC) karo na 13 a nan birnin Beijing, inda bisa ga kundin tsarin mulkin kasar, firaministan kasar Li Keqiang ya gabatar da sunayen wadanda ake shirin nada su a matsayin mataimakin firaministan kasar da mamban majalisar gudanarwa ta kasar da ministocin kasar da darektocin hukumomi daban daban da shugaban babban banki da shugaban hukumar kula da aikin binciken kudi, don taron ya dudduba.
Tawagar shugabanni kuma sun yanke shawarar gabatar da nadin ga tawagogin wakilai mahalarta taron don su yi nazari a kai.(Lubabatu)