in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi na sa ran taro tsakanin DPRK-ROK da tattaunawa tsakanin DPRK da Amurka za su gudana ba tare da tangarda ba
2018-03-13 11:02:18 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da babban mashawarcin shugaban kasar Koriya ta Kudu ROK kan harkokin tsaro Chung Eui-yong jiya Litinin a nan birnin Beijing.

Shugaba Xi Jinping ya yabawa takwaransa na Koriya ta Kudu Moon Jae-in, bisa turo mashawarcinsa da ya yi a matsayin wakili na musamman da zai masa bayani dangane da ziyarar da ya kai kasashen Koriya ta Arewa DPRK da kuma Amurka.

Ya ce, suna sa ran taron da Koriya ta Arewa da takwararta ta Kudu da kuma tattaunawar da Koriya ta Arewar da Amurka za su yi, za su gudana ba tare da wata tangarda ba, yana mai bayyana fatan za a cimma kwakkwarran ci gaba game da kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya da daidaitar dangantaka tsakanin bangarorin.

A nasa bangaren, wakilin na Koriya ta Kudu Chung Eui-yong, ya jinjinawa kasar Sin bisa rawar da ta taka wajen taimakawa ganin an samu kyawawan sauye-sauye game da batun zirin Koriya, inda ya ce, a shirye kasarsa take ta ci gaba da aiki kut da kut da kasar Sin domin dorewar ci gaban da aka samu yanzu dangane da zirin.

Har ila yau, shugaba Xi Jinping, ya ce a matsayin kasarsa ta makwabciyar zirin Koriya, kasar Sin za ta ci gaba da mara baya ga kasashen Koriya ta Kudu da ta Arewa wajen inganta dangantaka da sulhu da hadin kai a tsakaninsu.

Bugu da kari, ya ce kasar Sin tana goyon bayan Amurka da Koriya ta Arewa su fara tattaunawa tare da warware matsalar dake tsakaninsu.

Shugaba Xi Jinping ya kuma bayyana cewa, kasar Sin ta tsaya tsayin daka ne kan batun kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China