in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da wakilin musamman na shugaban Koriya ta Kudu
2018-03-12 20:01:53 cri

Yau Litinin ne a nan Beijing, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da Chung Eui-yong, wakilin musamman na shugaban kasar Koriya ta Kudu kuma shugaban ofishin harkokin tsaro na kasarsa.

A yayin ganawar, Xi Jinping ya nuna cewa, kasar Sin na sa ran shugabannin kasashen Koriya ta Kudu da ta Arewa za su iya ganawa da juna, kana za a yi tattaunawa yadda ya kamata a tsakanin kasashen Koriya ta Arewa da Amurka, sa'an nan za a iya samun hakikanin ci gaba a fannonin tabbatar da ganin an kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya da kuma farfado da hulda a tsakanin kasashe masu ruwa da tsaki yadda ya kamata.

A nasa bangaren, Chung Eui-yong ya ce, Koriya ta Kudu na fatan kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa, tana kuma son hada kai da Sin wajen ganin zaman tankiya a zirin ta ragu a halin yanzu, da kokarin ganin an warware batun nukiliyar Koriya ta Arewa cikin ruwan sanyi, a kokarin samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba a yankin. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China