in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin yana kan gaba cikin 'yan takarar neman shugabancin Rasha
2018-03-19 09:30:50 cri

Kwamitin harkokin zabe na tsakiya na kasar Rasha ya bayyana a yau cewa, bayan kidaya kuri'un da yawansu ya kai kashi 70 cikin dari bisa jimillar kuri'un da aka kada domin zaben shugaban kasar, shugaba mai ci Vladimir Putin, yana kan gaba sakamakon kuri'un da ya samu da yawansu ya wuce kashi 75.91 cikin dari.

Vladimir Putin ya nuna godiya ga masu kada kuri'a, saboda amincewa da suka yi da kokarin da Rasha ta yi, yana mai cewa zai kara kokarin daidaita kalubale da warware matsalolin da take fuskanta.

A yayin taron manema labaru da aka shirya a jiya da dare, Putin ya ce dukkan masu kada kuri'a a Rasha sun zama tsintsiya madauriki daya, kuma bisa kuri'un da suka jefa, ya gano cewa, sun amince da kokarin da Rasha ta yi a shekarun baya a cikin mawuyacin hali, kana sun yi ammana cewa Rasha za ta kara samun ci gaba, ya na mai cewa kasar za ta cimma nasara.

Bisa ka'idojin babban zaben shugaban kasar Rasha, wanda ya samu kuri'un da yawansu ya wuce rabin jimillar kuri'un da aka jefa ne zai zama shugaban kasar. Kwamitin harkokin zabe na koli na kasar zai tabbatar da sakamakon zaben kafin ranar 29 ga watan nan, zai kuma sanar da sakamakon a hukumance cikin kwanaki 3 bayan ya tabbatar da shi. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China