Bisa kididdigar da hukumar zaben kasar Rasha ta yi, jama'ar kasar ta Rashar kimanin miliyan 110 ne suka cancanci jefa kuri'u a zaben, kuma an kafa rumfunan zaben fiye da dubu 97, wadanda aka bude yau da safe da misalin karfe 8 kuma za a rufe su da karfe 8 na dare.
Hukumar zaben kasar Rasha zata tabbatar da sakamakon zaben kafin ranar 29 ga wannan wata, kuma za a bayyana sakamakon ne bayan da aka tabbatar da shi bayan kwanaki 3.
'Yan takara 8 ne suke fafatawa a zaben, ciki har da shugaban kasar na yanzu Vlładimir Putin, da dan takara na jam'iyyar kwaminis ta tarayyar Rasha Pavel Grudinin, da dan takara na jam'iyyar mai rajin samar da 'yanci da demokuradiyya ta kasar Rasha Vladimir Zhirinovsky da dai sauransu. (Zainab)