in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a ci gaba da dukufa wajen yin rigakafin gurbatar muhalli a Sin
2018-03-17 16:50:21 cri
Ministan harkokin kiyaye muhalli na kasar Sin Li Ganjie ya bayyana a yau Asabar cewa, ba a taba dakatar da ayyukan rigakafin gurbatar muhalli da kuma daidaita matsalolin gurbatar muhalli a kasar Sin ba, kana, a bana, za a gaggauta aiwatar da ayyukan kare muhalli.

Ya kara da cewa, daukar matakan kare gurbatar muhalli da daidaita matsalolin gurbatar muhalli a kasar Sin yana mai da hankali kan fannoni uku da suka hada iska da ruwa da kuma kasa. Sa'an nan, za a dukufa wajen cimma burin bisa fannoni uku da suka shafi kyautata yanayin muhallin halittu da rage karfin fitar da kayayyaki masu gurbata muhalli da kuma daukar matakan kariya da gudanar da bincike kan harkokin da za su gurbata muhalli. (Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China