in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta amince da shirin kafa tsarin kiyaye muhalli a yankuna 15 dake fuskantar barazana
2018-02-13 13:22:38 cri

Ma'aikatar kare muhalli ta kasar Sin (MEP) ta sanar da cewa, majalisar gudanarwar kasar ta amince da kafa wani tsarin kiyaye muhalli a wasu yankunan kasar 15 don dakile fargabar da yankunan ka iya fuskanta, da nufin karfafa shirin kare muhallin kasar.

Majalisar gudanarwar ta tsara shirin kare muhallin ne daga yankunan Beijing, Tianjin, Hebei, Ningxia, da kuma wasu yankuna 11 dake zirin tattalin arziki na Kogin Yangtze, kamar yadda Cheng Lifeng, shugaban sashen lura da muhallin halittu na ma'aikatar kare muhallin ya sanar.

Yankunan da aka ware don daukar matakan kariyar sun kai fadin murabba'in kilomita 610,000, ko kuma kashi daya bisa hudu na fadin lardunan 15 da aka kebe, in ji Cheng.

A shekarar da ta gabata ma, hukumomin tsakiya sun sanar da wasu ka'idojin kare muhalli ga yankunan da ake da fargabar fuskantar barazanar, a matsayin wasu dabarun kare muhalli a wadannan yankuna. Ana sa ran za'a inganta kyakkyawan tsarin kare muhalli a duk fadin kasar ta Sin nan da karshen shekarar 2020, kamar yadda ka'idojin suka nuna.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China