Binciken, wanda ake burin cimma alkaluman da aka yi kiyasa tun daga shekarar 2017, zai taimaka wajen tantance cikakkun alkaluman manyan hanyoyin dake haifar da gurbatar muhalli, wanda ya kunshi adadin masu gurbata muhalli daga bangaren masana'antu, da aikin gona, da bangaren wuraren zama, da kuma yadda za'a tunkari matsalar ta magance gurbatar muhalli.
Sakamakon da za'a samu daga binciken zai taimaka wajen kara sanya ido kan masu gurbata muhallin da kuma yadda za'a tabbatar da ingancin muhalli. (Ahmad Fagam)