in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin TAILG na Sin ya kulla hulda da hukumar kula da muhalli ta MDD
2018-03-14 09:16:50 cri
Kamfanin TAILG mai samar da ababen hawa masu aiki da lantarki na kasar Sin, ya sanya hannu kan wata yarjejeniya ta hadin gwiwa da hukumar MDD mai lura da kare muhalli, a wani mataki na fara samar da nau'in ababen hawa masu amfani da lantarki a Afirka da ma wasu sassa na duniya.

Daraktan tallace tallace na kamfanin Xu Rong, ya ce yarjejeniyar za ta taimakawa gwamnatocin Afirka, da ma sauran sassa na duniya, da wata dama ta fara raba kasashen su da ababen hawa masu fidda hayaki mai gurbata muhalli.

Mr. Xu ya ce hukumar ta MDD na shirin zabar kasashe 8 da za a fara gwajin wannan shiri da su nan gaba cikin wannan shekara ta 2018. Ya ce

baya ga shirin samar da horo, wakilai daga gwamnatocin kasashen Afirka, za su samu dama ta ziyartar helkwatar kamfanin na TAILG, don ganewa idanun su yadda yake gudanar da ayyukan sa.

Kamfanin TAILG dai shi ne na daga cikin jerin kamfanonin dake kera ababen hawa masu amfani da lantarki da ke kan gaba a nan kasar Sin, wanda kuma ke kera Babura da kekuna, da Babura na musamman, da kuma masu kafafu 3, wadanda dukkannin su ke amfani da lantarki.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China