Bisa ga alkaluman kididdigar da hukumomin suka fitar a lokacin taron shekara-shekara na wakilan jami'an tafiyar da harkokin mulkin birnin Beijing karo na 15 wanda ke gudana a halin yanzu ya nuna cewa, an samu karin yuan miliyan 590.
A cewar rahoton da mahukunta suka fitar game da kasafin kudin Beijing na shekarar 2018, za'a yi amfani da kudaden ne wajen magance hayaki mai gurbata muhalli da ake samu ta hanyar amfani da sinadarin kwal, da hayakin da ababen hawa ke fitarwa, kuma za'a kashe makudan kudade wajen maye gurbin sinadarin kwal zuwa nau'ikan makamashi mai tsabta a yankunan karkara. (Ahmad Fagam)