Jamie McGoldrick ya bayyana a jiya cewa, akwai mutane miliyan 21 dake neman agaji, kuma miliyan 7 daga cikinsu, na cikin halin yunwa inda suka dogara kacokan a kan tallafin abinci.
Ya bayyana haka ne ga MDD ta wayar tarho, daga Amman na Jordan, saboda toshe hanyar isa Sanaa, babban birnin Yemen da aka yi.
Ya ce ci gaba da rufe tashoshin ruwa da na jiragen sama da rundunar kawancen da Saudi ke jagoranta ta yi, zai kara ta'azzara matsanancin halin da ake ciki. Yana mai cewa a ganinsa, matakin na barazana ne ga rayukan miliyoyin mutane dake kokarin rayuwa.
Ya kuma jadadda jawaban manyan jami'an MDD dake cewa, rikicin Yemen da aka fara watan Maris na 2015, ya haifar da matsalar jin kai mafi muni a duniya.
Ita ma hukumar UNHCR mai kula da 'yan gudun hijira ta MDD, ta ce ta kadu da yanayin jin kai da ke kara lalacewa a Yemen. (Fa'iza Mustapha)