Ministan ilmi na kasar Sin Chen Baosheng ya bayyana cewa, a fannin kafa makarantun hadin gwiwar Sin da kasashen waje, har kullum gwamnatin kasar Sin na dora muhimmanci kan bin ka'idojin shigowar makarantun waje, da kafa irinsu na kasar Sin a ketare.
Ya ce ya zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta hada kai tare da wasu kasashen waje, wajen kafa hukumomin ba da ilmi da ayyukan koyarwa da yawansu ya zarce 2600.
Ministan ya fadi hakan ne a yau Jumma'a, a gun taron manema labarai na taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da ke gudana a nan birnin Beijing. Ya kuma kara da cewa, makasudin hadin kan Sin da waje shi ne, sassan biyu na iya koyi da juna don taimakawa juna a fannin ilmi domin amfanar jama'ar su, ta yadda yara Sinawa za su iya samun ilmi na gari daga ketare a cikin kasar su. Game da kasashen waje kuma, za su iya samun abun da suke bukata ta hanyar hadin gwiwa tare da kasar Sin.
Ya ce a nan gaba, za a dauki wasu matakai na sa kaimi ga ci gaban da ake buri a fannin. (Kande Gao)