An zartas da gyaran kundin tsarin mulkin kasar Sin bisa yawan kuri'un da aka kada
An zartas da gyaran kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin a yayin zaman taro na 3,na zagayen farko na taron majalisar wakilan jama'ar kasar karo na 13 da aka shirya jiya Lahadi a nan birnin Beijing. Haka zalika, an kara shigar da sabbin abubuwan cikin kundin wanda ya shafi gudanar da harkokin kasar Sin a sabon zamani bayan shekaru 14. A yayin taron manema labaru da aka shirya bayan taron, daraktan kwamitin kula da ayyukan dokokin shari'a na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Shen Chunyao ya bayyana cewa, gyaran kundin tsarin mulki wani muhimmin aiki ne da ya shafi harkokin siyasar kasar Sin, kuma wata babbar nasara ce da kasar ta cimma wajen raya dokokin shari'a bisa yanayin da ake ciki na raya gurguzu da ke da halin musamman na kasar Sin a sabon zamani. (Bilkisu)