Yayin da yake ba da jawabi a wajen bikin, sabon shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar Sin, mista Wang Yang, ya ce 'yan majalisar za su mai da ra'ayin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin na sabon zamani da shugaba Xi Jinping ya gabatar a matsayin babbar manufar da za su bi, da tsayawa kan zama karkashin jagorancin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da kokarin sauke nauyin dake bisa wuyansu, ta yadda za a samu damar kara kyautata aikin majalisar.
Mista Wang ya kara da cewa, tsarin hadin gwiwa tsakanin jam'iyyu daban daban, da na ba da shawara kan harkokin siyasa, wanda ake gudanar a karkashin jagorancin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, shi ne wata babbar manufar siyasa ta tushe ta kasar Sin. Wanda kuma ya kasance wani sabon nau'in tsarin jam'iyyun siyasa ne da jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da jama'ar kasar, da jam'iyyu daban daban na kasar suka kirkiro. A cewar jami'in, majalisar za ta dora muhimmanci kan manufar siyasa, da kokarin bauta wa jama'a, gami da kokarin kyautata aikinta na ba da shawara kan harkokin siyasar kasar Sin.(Bello Wang)