in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dokar sanya ido za ta baiwa JKS damar kyautata aikin yaki da rashawa
2018-03-13 12:14:48 cri

An gabatar da daftarin dokar sanya ido ga zauren majalisar dokokin kasar Sin don yin tattaunawa bisa mataki na uku kan dokar a yau Talata, da nufin samun ingantaccen dubi cikin tsanaki kan dokar karkashin shugabancin jam'iyyar mai mulkin kasar.

Sabuwar dokar, tana daga cikin muhimman sauye sauyen da hukumomin sanya ido na kasar Sin suka kuduri aniyar aiwatarwa, kuma ana sa ran dokar za ta kasance a matsayin wani ginshiki, kuma a matsayin wata muhimmiyar dokar da za ta taka rawa game da shirin yaki da rashawa na kasar Sin, da kuma bibiyar yadda ayyukan ke gudana a kasar, Li Jianguo, mataimakin shugaban kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC ta 12, shi ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake karin haske game da gabatar da dokar ga taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC ta 13 wanda ke gudana a halin yanzu.

Ya nanata cewa, dokar za ta kara kaimi ga jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS a shirinta na yaki da ayyukan rashawa.

A bisa wannan doka, za'a kafa sabbin hukumomin da za su dinga sanya ido a matakan tsakiya, da larduna, da birane, da sauran yankunan kasar ta Sin. Kuma an damkawa hukumomin alhakin gudanar da dukkan batutuwa dake da nasa da laifukan cin hanci da rashawa, za su gudanar da ayyukansu na sanya ido a matsayin masu cin gashin kansu, kana ba za su fuskanci duk wani katsa-landan daga bangaren gwamnati, ko wasu hukumomin al'umma, ko kuma daidaikun mutane ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China