Gwamnatin kasar Sin ta bayyana wani gagarumin shirin yiwa hukumominta garambawul, wanda zai samar kyakkyawan fasali da inganci da kuma nagartar aiki.
Za a mika shirin na garambawul na majalisar gudanarwar kasar ga taron farko na majalsiar wakilan jama'ar kasar ta 13 dake gudana domin ya yi nazari kansa.
A cewar daftarin shirin, bayan garambawul din, za a samu ma'aikatu da hukumomin majalisar gudanarwar guda 26.
Daga cikin sabbin ma'aikatun, akwai na kula da albarkatu da na harkokin gogaggu kan aiki da kuma ma'aikatar kai agajin gaggawa.
Sauyin wanda ke da nufin sake fasalin ma'aikatu a wasu muhimman bangarori zai kara karfafa ayyukan gwamnati ta fuskar kula da tattalin arziki da sa ido kan harkokin kasuwanni da kula da al'umma da ayyukan gwamnati da kuma kare muhallin hallitu da na tsirrai. (Fa'iza Mustapha)