Zaman na hudu na zagaye na farko na taron majalisar NPC karo na 13 da ya gudana a jiya, ya samu halartar Shugabannin kasar Sin da suka hada da Xi Jinping da Li Keqiang da sauransu.
Wakilan jama'ar sun amince da samar da kwamitoci na musammam ga majalisar ta 13, tare da zabar shugabanni da mataimakansu da kuma mambobi.
Bisa matakin da suka dauka, majalisar karo na 13 za ta kunshi kwamitocin musammam guda 10, wadanda za su mayar da hankali kan bangarorin da suka shafi harkokin kabilu da na kundin tsarin mulki da dokoki da harkokin kasashen waje da kare muhalli da harkokin noma da kuma na karkara.
Yayin taron na jiya, wakilan sun amince da jerin sunayen shugabanni da mataimakansu da kuma mambobin kwamitin kula da dokoki da kundin tsarin mulki da na kwamitin kula da harkokin kudi da tattalin arziki. (Fa'iza Mustapha)