Hukumar kula da masana'antu da harkokin cinikayya ta majalisar gudanarwar kasar Sin (SAIC) ta bayyana hakan a Alhamis din nan, yayin bikin ranar kare hakkin masu amfani da kayayyaki na duniya, inda ta wallafa wasu sabbin bayanai a shafinta na intanet game da yadda za a rika sauraron korafe-korafen masu sayen kayayyaki da tattaunawa game da ingancin kayayyakin da ake samarwa. Kuma daga lokaci zuwa lokaci za a rika yi musu bayani. (Ibrahim Yaya)