in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin kudin da aka samu daga kasuwanci ta yanar gizo a kauyukan Sin ya kai yuan biliyan 900 a bara
2017-10-13 09:26:05 cri

An kaddamar da taro karo na 2, kan kasuwanci ta yanar gizo da aka gudanar a kauyukan kasar Sin jiya Alhamis a birnin Lishui na lardin Zhejiang dake kudu maso gabashin kasar, inda aka fitar da wani rahoto mai taken "ci gaban kasuwanci ta yanar gizo a kauyukan kasar Sin tsakanin shekarar 2016 da ta 2017".

Rahoton ya bayyana cewa, a shekarar 2016, jimilar kudin da aka samu daga kasuwanci ta yanar gizo a kauyukan kasar Sin ya kai RMB yuan biliyan 894.54. Sannan, sayayya ta yanar gizo a kauyukan kasar ta samar da guraben aikin yi sama da miliyan 20 ga al'ummun kasar.

Rahoton ya kuma bayyana cewa, ko shakka babu kasuwanci ta yanar gizo a kauyukan kasar yana taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arzikin kasar.

Jami'in dake aiki a cibiyar kasuwanci ta yanar gizo ta kasa da kasa ta kasar Sin ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, sayayya ta yanar gizo a kauyukan kasar Sin ta karu cikin sauri, ya na mai cewa, tana ba da gagarumar gudumuwa ga aikin yaki da talauci a kauyukan kasar.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China