Alkaluman da ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta gabatar a yau Jumma'a ya nuna cewa, a cikin watanni 9 na farkon shekarar da muke ciki, kasar Sin ta yi amfani da jarin waje da yawansa ya kai kudin Sin yuan biliyan 618.57, wanda ya karu da kashi 1.6 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekarar bara. Haka kuma an kafa sabbin masana'antu masu jarin waje guda 23541 a fadin kasar ta Sin, adadin da ya karu da kashi 10.6 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara.
Mista Ye Wei, mataimakin shugaban sashen harkokin jarin waje na ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya ce, nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da zurfafa yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, raya shiyyoyin gwaji na yin ciniki ba tare da shinge ba yadda ya kamata, kafa shiyyoyin bunkasa tattalin arziki da dai sauransu domin jawo jarin waje, da mayar da hankali wajen kyautata yanayin kasuwanci, a kokarin inganta karfin yin takara ta fuskar jawon jarin waje. (Tasallah Yuan)