in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
PSG ce ta dace da Neymar in ji mahaifin sa
2018-03-15 14:45:39 cri

Mahaifin tauraron kwallon kafar Brazil dake wasa a PSG wato Neymar, ya ce kulaf din da dan na sa yake takawa leda a yanzu haka, shi ne mafi dacewa gare shi.

Neymar Senior ya bayyana hakan ne yayin da yake karyata rade radin da ake yi, cewa dan na sa baya jin dadin zama a kungiyar ta PSG, kuma wai mai yiwuwa zai koma kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.

Neymar Senior wanda kuma shi ne manajan dan na sa, ya ce PSG ce gida ga dan na sa a yanzu da ma nan gaba.

A baya bayan nan ne dai mahaifin dan wasan ya yi tattaki tare da jagoran kungiyar ta PSG Nasser Al-Khelaifi, da daraktan wasanni na kungiyar Antero Henrique, inda suka kai ziyara cibiyar tallafawa harkokin wasanni ajin matasa dake Praia Grande a kudu maso gabashin kasar Brazil.

Gabanin hakan sun ziyarci Neymar, wanda yake jiyya a katafaren gidan sa dake Mangaratiba, kusa da birnin Rio de Janeiro. Neymar mai shekaru 26 da haihuwa, na farfadowa daga wani rauni da ya ji a kafar sa ta dama.

Da yake tsokaci game da waccan jita jita, shi ma Al-Khelaifi ya karyata yiwuwar barin Neymar kungiyar ta PSG. Ya ce dan wasan na cikin farin ciki a kungiyar da yake takawa leda, yana kuma fatan murmurewa domin gaggauta komawa buga wasanni.

An dai yi hasashen cewa Neymar ba zai koma taka wasa ba har sai bayan watan Mayu, wanda hakan ke nufin ba zai buga wa PSG ragowar wasannin ta na kakar bana ba. Kaza lika sai sa'a ya samu damar halartar gasar cin kofin duniya da za a buga a Russia tun daga ranar 14 ga watan Yuni dake tafe.

Bayan zuwan sa PSG daga Barcelona, Neymar ya ci wa kungiyar ta sa ta yanzu kwallaye 28, ya kuma taimaka wajen cin wasu kwallayen 16.

PSG ta yi cinikin Neymar kan zunzurutun kudi har Euro miliyan 222 a watan Agustar bara, a wani ciniki da ya karya matsayin bajinta a tarihin cinikayyar 'yan wasan kwallon kafa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China