Ana zargin karancin kudade da rashin tafiyar da harkokin wasannin kasar yadda ya kamata ne ya haddasa soke wasan. Kungiyar wasan Harambee Stars zata ziyarci Morocco, inda zasu taka leda da jamhuriyar Afrika ta tsakiya a wani wasan na sada zumunta da za'a buga a ranar 27 ga watan Maris.
Babban jami'in hukumar kula da wasannin kwallon kafar Ghana Robert Muthomi ya sanar da cewa an soke wasan ne bayan da Gambian ta gaza samar da kudaden da zata biya kudin jirgi ga tawagar 'yan wasan kasar zuwa birnin na Marrakech.
Muthomi yace "Ba zai yiwu ba, ba zamu buga wasa da Gambia ba. Kungiyar wasan kwallon kafan Gambia bata da kudin jirgi zuwa Marrakech. Tilas ne mu canza wasanmu".
Raoul Savoy, kociyan kungiyar wasan jamhuriyar Afrika ta tsakiya, ya bada tabbacin shirye shiryen da suke na gudanar da wasan.
"Ina bada tabbacin zamu buga wasan sada zumunta na biyu daidai da ranar da hukumar FIFA ta tsara. Za'a buga wasan ne a ranar 27ga watan Maris a Marrakech, na kasar Morocco," inji Savoy kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Sannan ya bada tabbacin cewa bangarensa zai buga wasan da Gambia kafin fafatawa da Kenya.(Ahmad Fagam)