in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tevez ya zura kwallon farko ga Boca tun bayan komawar sa kungiyar
2018-02-07 19:39:09 cri
Carlos Tevez ya ciwa kungiyar Boca Juniours kwallon sa ta farko, tun bayan komawar sa kungiyar daga Juventus a watan da ya gabata.

Tevez ya ci wa kungiyar kwallon ne, yayin wasan ranar Lahadin karshen kamon jiya, wanda suka buga da kungiyar San Lorenzo, wasan da suka tashi kunnen doki 1 da 1.

Sakamakon wasan dai ya baiwa Boca damar wuce kungiyar San Lorenzo da maki 6 a teburin gasar Superliga ta kasar Argentina, bayan kungiyoyin biyu sun kammala wasanni 14.

Tevez, wanda ya fara taka leda a kungiyar Boca a shekarar 2001, ya kuma buga wasa a kulaflikan Corinthians, da West Ham, da Manchester United, da Manchester City da Juventus, kafin ya komawa Boca dake birnin Buenos Aires a shekarar 2015.

Daga bisa ni kuma, bayan rashin nasara da kungiyar sa ta Shanghai Shenhua ta kasar Sin ta ci karo da ita a karar wasa ta bara, Tevez ya sake komawa Boca a karo na uku.

A sauran wannin da aka buga na gasar Superliga a ranar Lahadi, Gimnasio La Plata ta yi kunnen doki maras ci da kungiyar Arsenal de Sarandi, kana kungiyar Estudiantes ta doke Newell's Old Boys da ci 4 da 2. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China