in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai horas da 'yan wasan Zambia ya zabi wadanda zasu halarci gasa tsakanin kasashe 4
2018-03-15 14:43:11 cri
Wedson Nyirenda, shugaban babbar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Zambia, ya zabi 'yan wasa 30 da zasu halarci gasar wasanni tsakanin kasashen Afrika 4, kamar yadda hukumar gudanar da wasanni ta kasar ta sanar a ranar Asabar.

Kasar Zambian ne zata karbi bakuncin gasar wasannin, wanda ya kunshi kasashen Angola, Afrika ta kudu, Zimbabwe sai kuma ita kanta Zambiyar mai masaukin baki, za'a fafata ne a wasannin tsakanin ranakun 21-24 ga watan nan na Maris a katafaren filin wasa na Levy Mwanawasa dake Ndola, a lardin Copperbelt.

Manajan watsa labarai na kungiyar wasan kwallon kafan kasar Zambia (FAZ) Desmond Katongo, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda yace tawagar 'yan wasan da aka zaba zasu halarci wani shirin samun horo tun daga ranar 11 ga watan nan na Maris domin tunkarar wasannin da za'a buga.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China