in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sao Paulo ta nada Aguirre dan kasar Uruguay a matsayin koci
2018-03-15 14:42:15 cri
Sao Paolo ta ayyana sunan tsohon dan wasanta Diego Aguirre a matsayin sabon shugaban kungiyar wasanta bayan da ta sallami Dorival Junior.

Dan wasan mai shekaru 52 da haihuwa dan asalin kasar Uruguay ne zai karbi shugabancin kungiyar wasan ta Tricolor a karon farko bayan wasan su na Copa do Brasil da suka buga da CRB a ranar Laraba.

Manajan wasan kwallon kafan kungiyar Rai ya wallafa a shafin yanar gizo na kungiyar wasan, inda ya bayyana Aguirre a matsayin kocin zamani wanda ya nuna kyakkyawan sakamako. Yace ana fata salon da yake amfani dashi zai dace da kulub din nasu.

Aguirre ya bar aiki ne tun bayan da ya sake aikinsa na kociyan kungiyar wasan San Lorenzo na kasar Argentina a watan Satumbar bara. A karo 6 yana wakiltar kungiyar wasan Brazilian Serie a matsayin kwararren dan wasa a shekarar 1990, inda ya samu nasarar zara kwallaye 3 a wasanni 8.

An sallami Dorival Junior ne daga aiki bayan da Tricolor ta tashi da ci 2-0 a hannun abokiyar karawarta Palmeiras a wasan cin kofin kwararru na jahar Sao Paulo a ranar Alhamis din data gabata. Dorival shine manajan kungiyar wasan Sao Paulo na 6 da aka sallama daga aiki a cikin kasa da shekaru 3.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China