Dan wasan mai shekaru 31 da haihuwa ya fuskanci takunkumin hana shi taka leda a wasannin kasa da kasa na watanni 9, da kuma wani takunkumin na watanni 4 ga duk wasu sauran wasanni, bayan da ya ciji dan wasan kasar Italiya Giorgio Chiellini a gasar rukuni da suka buga a Natal.
Suarez ya ce ya shirya fuskantar aikin kammala wannan kakar wasanni ta bana tare da Barcelona, kuma zai tabbatar da ya nishadantar da 'yan kasar sa a gasar cin kofin duniya ta bana, bayan abun da ya faru a shekarar 2014.
Uruguay dai za ta kece raini da kasashen Masar da Saudi Arabia, da kuma mai masaukin bakin gasar cin kofin na duniya wato Rasha, a gasar da za a gudanar tsakanin ranekun 14 ga watan Yuni zuwa 15 ga watan Yulin wannan shekara.
Tuni dai Suarez ya ciwa Barcelona kwallaye 16, a wasannin gasar La Liga 18 da ya buga a kakar bana, ya kuma ce Uruguay ba za ta ragawa duk wata kungiya da ta hadu da ita a gasar cin kofin na duniya na bana ba.
Ya ce wasu kungiyoyin sun yi suna a gasar cin kofin duniya, amma hakan ba ya nuna cewa sun fi kungiyar sa karfi ta fuskar kwarewar 'yan wasa ko mai horaswa. A baya kungiyar sa ta ci karo da rashin nasara, amma sun koyi darashi daga hakan, kuma sun samu karin karfin gwiwa yadda ya kamata.
Suarez ya kuma bayyana rashin jin dadin rabuwa da kyaftin din kungiyar kasar sa Diego Lugano, wanda ya yanzu haka ya koma kungiyar Sao Paulo ta Brazil a matsayin jami'in gudanarwa.(Saminu Alhassan)