A wasan da aka buga a katafaren filin wasa na Grand Stade na birnin Tangier na kasar Morocco a ranar Juma'a, dan wasa Thierry Manzi ya kasance a matsayin gwarzon dan wasa a wasan, wanda ya samu nasarar zara kwallo bayan mintoci 67 da fara wasan, dan wasan ya kware matuka wajen buga kwallo da ka, lamarin da ya bashi damar samarwa Rwandan maki uku nan take.
Nasarar dai ta daga matsayin kasar Rwanda zuwa rukuni guda da Najeriya wato rukunin C da maki 4, sai kuma Libya wanda ke bi musu baya da maki 3.
A halin da ake ciki, kungiyoyin wasanni 3 ne zasu kara a wasan kusa dana karshe, a rukunin C.
A ranar Talata, Rwanda zata kara da Libya yayin da Najeriya zata taka leda da Equatorial Guinea.
A rukunin A Morocco da Sudan zasu kara, sai kuma Zambia da Namibia zasu kara a rukunin B, kuma tuni an riga an kammala tsara samar musu da gurabe a wasan kusa dana kusan karshe cikin wannan mako bayan sun samu nasarar lashe wasanninsu biyu na farko.
Wasannin dai na kwallon kafan 'yan kasashen Afrika ne na sada zumunta, wadanda ya kunshi kungiyoyin wasa 16 a rukunoni 4.
Daga kowane rukuni, kungiyoyi biyu dake kan gaba ne zasu halarci wasan kusa na kusan karshe.(Saminu Alhassan)