Dan shekaru 17 da haihuwa, Vinicius Junior wanda ke sanye da riga mai lamba 10 a Flamengo, ya ciwa kungiyar ta sa kwallon da ita ce raba gardamar wasan. Yanzu haka dai ya riga ya ci kwallaye 37 a wasannin da ya bugawa Flamengo, tun fara takawa kungiyar wasa a watan Janairun bana.
Vinicius Junior shi ne dan wasa mafi tsada cikin matasan 'yan wasa da Real Madrid ta saya a watan Mayun bara, inda ta yi cinikinsa kan kudi har Euro miliyan 45.
A baya an shirya komawar sa Madrid a watan Yuli dake tafe, kafin daga bisani Flamengo ta daidaita da Real Madrid, game da amincewa dan wasan ya ci gaba da taka mata leda zuwa shekara mai zuwa.(Saminu Alhassan)