in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon kocin Chile ya sha alwashin yaki da rashin da'a tsakanin 'yan wasa
2018-01-25 14:54:22 cri
Sabon kocin tawagar 'yan wasan kwallon kasar Chile Reinaldo Rueda, ya yi kira ga 'yan wasan kungiyar da su kasance masu da'a da martaba juna, musamman a wannan gaba da suke fatan farfadowa daga rashin nasarar su, ta neman gurbin buga gasar cin kofin duniya da hukumar FIFA ke shiryawa.

Koci Rueda mai shekaru 60 da haihuwa ya gana da 'yan jaridu a ranar juma'a a karon farko, tun bayan da ta bar horas da kungiyar Flamengo ta Brazil a ranar 8 ga watan Janairun nan.

Kungiyar kasar ta Chile dake rike da kofin zakarun nahiyar ta wato Copa America, ta kasance ba bu mai horaswa, tun bayan da Juan Antonio Pizzi ya ajiye aiki, biyowa bayan rashin nasarar samun gurbin buga gasar cin kofin duniya da kungiyar ta yi.

To sai dai sabon kocin kungiyar ya ce duk wasu abubuwa da suka faru a baya sun wuce, yanzu dole 'yan wasan na Chile su dage su baiwa marada kunya.

Da aka tambaye shi game da rashin da'a da ake zargin wasu 'yan wasan kungiyar na aikatawa, sabon kocin ya ce yana jan hankalin su da su nutsu, su martaba tawagar kasar su, kuma ba abun da zai ce ga wadanda ba za su karbi wannan shawara ta sa ba, illa Allah raka taki gona.

Koci Rueda wanda ya taba horas da kungiyoyin kasashen Colombia, da Ecuador da Honduras, ya kulla kwangilar shekaru 4 da Chile, bisa sharadin tsawaita wa'adin ta idan har da bukata.

Rueda ya ce burin sa 2 ne a Chile; wato lashe kofin Copa America na shekarar 2019 a Brazil, da kuma samarwa kungiyar gurbin buga gasar cin kofin duniya na shekarar 2022 da za a yi a Qatar.

Rahotanni na cewa cikin makwanni masu zuwa, kocin zai ziyarci 'yan wasan Chile dake sassan nahiyar Turai da Mexico, gabanin wasan sada zumunta da ake shirin gudanarwa tsakanin Chile da kasashen Sweden da Denmark. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China